Yadda ake faten wake da doya

0
982

Barkanmu da  kasancewa a fannin girke girken mu na wiki hausa, zamu koyi yadda ake faten wake da doya tare dani Hafsat Shettima.         

Abubuwan haɗawa
 • Wake (½ kofi)
 • Doya peeled and washed (gwargwadon buƙata)
 • Attaruhu Jajjagaggen 5 (ko gwargwadon buƙata)
 • Jajjagaggen Tattasai 2
 • Jajjagaggen Albasa 2
 • Kifi busasshe
 • Cray fish niƙaƙƙe
 • Manja
 • Ogu leave Yankakken
 • Maggi
 • CurryJajjagaggen Tafarnuwa
Yadda ake haɗawa
 1. Da farko za’a dafa wake ya nuna sai a ajiye gefe.
 2. A cikin wata tukunya mai zurfi a saka manjan sannan a yanka albasa ya ɗan fara soyuwa, sai ki zuba kayan miyanki, maggi, curry da tafarnuwa idan ya soyu saiki zuba ruwa yaɗan tafasa.
 3. Sai ki zuba doya da ogu da kifi sannan a rufe yayi kamar minti 10-15 ko kuma idan doyar tayi laushi sai ki zuba wake a juya. A yi a hankali wurin juyawa kar waken ya farfashe.
 4. A barshi na minti 4-5 sannan a sauke.
 5. Aci da fanke ko a haka.
Domin koyan Yadda ake farfesun kayan ciki a sauƙaƙe danna wannan koren rubutun