Hanyoyi 11 da ake rage kiba ba tare da an kashe ko sisi ba.

0
2663

1. Ka tabbatar ka Karya kumallo a kowacce rana, domin kin karin kumallo ba zai taimaka maka wajen rage kiba ba, sai dai ma ya Hana ka samun kuzari a tsawon ranar da ba ka yi Karin kumallon ba.

2. Ka ci abinci na yau da kullun. Domin hakan yana taimakawa wajen ƙone sinadarin (calories) a cikin sauri a lokutan da rana ta take.

3. Ka ci ‘yayan itace da ganyayyaki a mafi yawan lokaci, domin ‘Ya’yan itace da ganyayyaki suna da ƙarancin sinadarin kiba wato (fat).

4. Ka Kara yawan motsa jiki ko ayyukan da ka ke yi na yau da kullum.

5. Ka Sha ruwa Mai yawa, Kuma ka da ka bar kishirwa a tare da Kai.

6. Ku ci abincin da ke ƙunshe da (fiber) mai yawa, hakan zai taimaka maka jin ƙoshin lafiya, da rage maka teba da rage nauyi. Ana samun fiber a cikin abinci daga tsirrai, irin su ‘ya’yan itace da ganyayyaki, hatsi, da shinkafa da taliya, da wake.

7. Ka guji cika cikin ka da abinci, a maimakon haka sai ka rinka hakura da abincin kafin kaji ka koshi. Domin ciki na daukar kimanin mintuna 20 kafin ya gayawa kwakwalwa ya koshi.

8. Kada ka haramtawa kanka abincin da kake so, a maimakon haka kawai sai ka rage yawan cin sa.

9. Ka musanya cin kayan kwalam da makulashe izuwa cin ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki.

10. Ka guji Sha ko cin abin da ke da sinadarin giya a ciki

11. Ka tsara wa kanka lokacin cin abici.