Inganta Rayuwar Ma’aurata Ta Hanyar Karin Magana

0
300
INGANTA RAYUWAR MAAURATA TA HANYAR AMFANI DA KARIN MAGANA
A cikin wani littafi da na rubuta mai suna,“Kimiyya da fasahar zaman aure’ na yi wani fasali da na kawo karin magana guda dari da ashirin da takwas a cikinsa wadanda nake ganin da ma’aurata za su yi amfani da su a rayuwarsu ta aure da sun warware masu matsaloli masu yawa,da kuma sun zauna lafiya cikin jin dadi da rufin asiri.
Ganin irin muhimmancin karin magana a kowane sashe na rayuwa na ga ya kamata na dan tsakuro kadan daga cikinsu domin fadakarwa da hannunka mai sanda ga yan’uwa musamman ma’aurata.
1.GANI GA WANE YA ISHI WANE TSORON ALLAH
_GANIN BUZU A MASALLACI YA ISHI AKUYA TSORON ALLAH
Tsokaci
Ya kamata idan wani ya yi wani kuskure a zaman aurensa ,mace ko namiji,kuma har wannan kuskuren ya haifar da damuwa da bacin rai da nadama da wani mummunan sakamako ga ma’aurata, to ku ma ku kaucewa aikata irin wannan kuskuren , wannan ya zama wa’azi a gare ku.
2.YANZU YANZU SAI ALLAH
Tsokaci
Duk abinda kuke so ko kuma wanda ba kwa so, ba za ku iya tabbatar da shi ko kawar da shi nan take ba, dole sai a hankali,saboda cuta lokaci guda take shiga ,amma waraka sai a hankali.kuma barna ce ake yin ta yanzu amma gyara sai an dauki lokaci.Sai ka ga an yi shekaru ana gini amma a yan awannin sai a iya rusa shi, a sake wasu shekarun ba sake gina shi ba.
3.BA A BARI A KWASHE DUKA
In dai aka yiwa rayuwar aure sartse kamar aka yi saki aka dawo,ko aka yi wata hatsaniya aka daidaita ,to fa yana da wahala a koma kamar yadda ake a da.Saboda haka a guji abinda zai kawo fitina a rayuwar aure ,In kuma ta faru,an daidaita ,to sai a yi hakuri da abinda ya samu.
Misali wacce rikici ya kai har sai da aka sake ta aka auri wata sannan aka dawo da ita ,to ka ga ai ta rasa matsayinta na uwargida,kuma In ta ce lallai sai ta koma kamar yadda take a da ,to fa kamar tana neman daukar Dala ne ba gammo.
4.HANA WANI HANA KAI
Tsokaci
Kada garin fushi ka hana matarka hakkin ta,ko ki hana mijinki hakkinsa.Misali ki ce ba za ki yi abinci ba,ko kai ka ce ba za ka ba ta abinci ba,saboda yin hakan ba zai damu wanda aka yi don shi din kadai ba, a’a har shi ma wanda yayin sai abin ya dame shi.Saboda haka kada a je garin ramuwa a rame.
5.ALLAH ƊAYA GARI BAMBAN
Ya kamata ma’aurata su fahimci halayen junansu,su yi hakurin zama da halin juna,saboda Allah bai yi mutane daya ba,kuma In ka san halin mutum ka sha maganin zama da shi.
Bari In tsaya a nan ,sai a fadada tunani,Ni kam sai wani jikon wai kare ya zubar da tsamiyar kura.