KARSHEN ALEWA

0
603
Halin da muke ciki a yanzun yakai matakin innalillahy wa”inna ilairaji”un idan ka cire maganar addini gaba dayanta kadawo da lamuran rayuwar nan akan mizanin hankali sai kaga babu wani sauran nishadi Ko kuma jin dadi daya rage maka indai a wannan duniyar da muke ciki kake.
Duk kuwa da irin damammakin da muka samu na cigaban, daya zo mana wadda yake sauqaqa mana rayuwa ba kamar zamanin iyayenmu da kakanninmu da suka gabata ba duba da cewa a wannan zamanin inda ka ‘dauke amana tausayi da jin qan juna babu abunda suke dashi na more rayuwa, basu da lantarki basu da ruwan famfo Kai hatta gine-ginen gidajensu ma indai ba na mai sarauta ko mai hannu da shuni bane ba wani qawatashi ake ba, amma haka bai hana musu rayuwa cikin aminci da yalwatacciyar lapiyar jiki data ruhi ba lapiya mai dorewa.
Amma yan uwa wani daga cikinku ya ta’ba tunanin abunda yasa iyayenmu suka fimu qarko? Dalilan suna da yawa amma ka’dan daga cikinsu mutumin shekara sittin zuwa saba”in baya Ko da shi kafiri ne zaka sameshi da ingantacciyar zuciya, kamala, da wadatar zuci bazaka ta’ba samunsa da qaryaba, bazaka ta’ba samunsa da cin amana ba, sannan jikin matayensu kullum lullube yake kirif! Balle Kuma musulmi idan ka lura cutuka da daman gaske shekarun baya babu su yanzun meya kawo su? Yawa-yawan alfasha, mutum bai ji tsoro Ko kunyar wadda ya halicce shi bama balle Kuma abokin halittarsa.
Idan ka juya wani janibin kuma mazaje sun kasa sauke nauyi da Allah ya ‘dora musu ba domin basu dashi ba a”a domin tunanin a hakan dukiyar zata taru. Kai subhanallhi, wa”iyazubillahi Allah ta”alah da kanshi yace ya zare hannayensa ga duk magidanci da bai sauKe nauyin kansa ba.
‘Dan uwa wanene yabaka ne? Allah ne fa Koh? To ya barka da wayonka taya kake ganin samun dacewa? Wani matakin lalacewa da matasa muke akai yanzun wai neman auren ma za”ay Amma sai an sanya haramci cikinsa bazai ta’ba yiwuwa a yi shi cikin tsabtaba.

Dayawan matsaltsalu da yara suke bawa iyayensu ya samo asali ne daga tushen yadda suka mallaki yaran.

A wata fuskar kuma yaran nasu ne amma ba halalin su ba kunsan dalilina? Tun kafin a auri uwar aka samu cikin yaron kuma akan cikin aka daura auren bayan an haife cikin Kuma ba”a daddara ba aka ci gaba da zaman zinar da ake ‘dan uwah ka sa’bawa Allah daya halicceka taya kake tunanin ‘ya’ya daka haifesu ba ta hanyar halali ba zasu yi maka biyayya? A irin hakane zakaji yaro ya kashe ubansa a”a wani yayi zina da uwarsa da dai sauran bala”o”i iri- iri da muke fuskanta a wannan Karnin.
Wannan dalili da wasu daga cikin mazaje suka ginu akai ya jawo babbar musibar da take addabar al”ummarmu a yau.
Maigida cikin kashi dari na nauyin da Allah ya dora maka baka sauqe kashi saba”in ba Kuma kanada tabbacin babu wani wadda zai yi maka dole sai kai din baka tunanin halin da uwa zata shiga? A qoqarinta na neman mafita har ta fada hallaka Kuma Kai Kaine ummull-aba”seen ‘din faruwar komai, Eh to hallaka mana a cikin nauyin da Allah ya dora muku babu wadda idan babu shi za”ay haqury, bazai ta’ba yiwuwa a rayu babu abinci ba, ko babu sutura, ko wajen kwanciya, ko kuwa magani a ciki dukka babu wadda za”ay haqury dashi dukkaninsu lamura ne na dole.
Kana tunanin idan ta samu mai bata abinci bazata kar’ba bane? Yau da gobe yana bata sau ‘daya idan ya bijiro da buqatarsa ko da wace iri ce zata amsa hannu bibiyu Ko ‘dan gudun rashin wadda zai bata. Wanene silar hakan?
Idan Kai matashi ne a wannan qasar bansan abunda yayi maka dadin da zaka ‘bata lahirarka ba bayan Kuma baka mori duniyar ba. Eh mana kaso saba”in na matasanmu basu da aikin yi, basu da wani mafarki akan gobensu Kuma bamu da wata madogara da muka jingina rayuwarmu a jiki. Matasa kunnenku nawa? Wallahy wankin hula yana gab! Da kaimu dare idan har mu bamu gyara ba a haka yaranmu zasu tashi suma haka nasu yaran abu yazo ya zame mana al”ada.
Eh al”ada mana ina dai itace akeyinta yau da gobe? Kuma babban abun takaicin a ce wai mun sunnatawa ‘ya’yayenmu abunda bazai kaisu tudun muntsira ba.

Eh kwarai da gaske dani daku ay munsan abunda muke aikatawa ba tone-tone. ‘dan uwa ko iyaye mahaifan mu kawai sukayi basu da ikon tsara mana yadda goben mu zata kasance.

Mune muke da damar zama abunda muke so kodai mu zama lalatattu Ko kuma nagartattu. Bamu da lokaci isashshen da zamu ‘batashi wajen sa’bon Allah ta”ala saboda komai yazo qarshe mu muka zo, eh mana alamomin tashin duniyah babu wadda bai bayyana ba ‘baro-‘baro.
Muyi amfani da lapiyarmu, da lokacinmu da iliminmu da dukkanin damar da muka samu domin samar da tsabtatacciyar al”umma ta hakane duniya bazata manta da sunayenmu ba ko qasa tayi mana hijabi da ita.
‘Dan uwa bakada lokacin ‘batawa kayi gaggawar miqa lamuranka ga mahaliccinka yi kokari ku rabu lapiya da iyayenka, hanzarta ka sauqe nauyin iyalanka duk azabar da zakaci wajen yin hakan domin ta hakane kadai zamu sadu da mahaliccinmu cikin salama!
Don Allah muso juna, muyiwa juna uzuri, Kuma mu yafi juna mu gina ingantacciyar rayuwa ko ba don komai bama domin amfanin kawukanmu.

Fatana Allah ta”ala ya jibanci dukkanin lamuranmu..

Budaddiyar wasika zuwa ga iyaye mata domin karanta wannan wasika danna kuren rubutun