Maganin Damuwa

0
297
MAGANIN DAMUWA
Wani bincike da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gudanar a farkon wannan shekarar 2020 ya tabbatar da cewa kimanin mutane miliyan 264 a duniya suna fama da cutar damuwa.Kuma kusan mutane dubu 800 ne suke mutuwa ko su kashe kansu a kowace shekara saboda damuwa.
Damuwa cuta ce ta ƙwaƙwalwa wacce take haifar da matsanancin baƙin ciki da bacin rai da fargaba da rashin jin dadin rayuwa da amincewa kowa.
Wanda ya kamu da wannan cuta sai ya rasa abinda zai yi ya ji dadin rayuwarsa , wannan ne ya sa wasu suke kashe kansu wai don su huta.
Babban abinda yake haifar da damuwa shine bakin ciki kan abinda ya wuce da wanda ake ciki da kuma fargaba da tsoron abinda ake zaton zai faru nan gaba.Wato In mutum ya tarawa kansa bacin ran jiya ya haɗa da na yau ga kuma tunanin gobe ma haka za a tashi ,to dukkanin rukunan cutar damuwa sun tabbata ga mutum.
A musulumci babu wata cuta da ba ta magani sai mutuwa.Kuma maganin musulumci kan kowane irin ciwo shine kat kuma kaifiyya.
Musulunci zai ba ka riga-kafi,ya bayyana maka dalilan da suke jawo ciwo da maganinsa da kuma yadda za a yi amfani da shi a warke da iznin Allah.
Ga waɗansu takaitattun bayanai da za su taimaka wajen magance damuwa da bacin rai In sha Allahu.
DALILAN DAMUWA DA MAGANI TA
1.RASHIN GODIYAR ALLAH TAALA DA WADATAR ZUCI
Sau da yawa In mutum ya rasa wani abu da yake da shi ko kuma bai samu abinda yake so ba,sai ya mance da duk wata niima da Allah ya yi masa,ya rinka jin shi rayuwarsa ba ta wani amfani.Wani ma abinda yake so din ba ya cikin lalurar rayuwa,kuma babu rufin asirin da bai samu ba, amma duk da haka sai ya damu kansa da kunci saboda bai samu yadda ransa yake so ba.
Maganin wannan shine mutum ya godewa Allah bisa niimomin da ya yi masa wadanda ba za su kirgu ba,ya rinka duban na kasa da shi ,kada ya rinka hangen na sama da shi.
Wannan zai haifarwa mutum wadatar zuci da samun gamsuwa da yanayin da ake ciki
.
2.RASHIN YARDA DA HUKUNCIN ALLAH TAALA
Allah Taala shine mai iko akan komai shine mai yin yadda ya so a lokacin da ya so ga wanda ya so,ta yadda ya so.Rashin yarda da haka yakan jefa mutum cikin damuwa maras iyaka.
Maganin wannan shine cikakkiyar yarda da amincewa da dukkanin hukuncin da Allah ya ƙaddara kanka ko ga waninka koda kuwa ba haka kai kake so ba,saboda shi Allah Taala ba a sa shi,ba a hana shi, ba a ce masa ga yadda zai yi,kuma ba a tashin hukuncinsa.
3.KANGAREWA KA’IDODIN RAYUWA
Allah Taala ya tsara rayuwar duniya kan waɗansu dokoki da tsare tsare wadanda a kansu take tafiya.
Duk wanda ya bi wadannan dokoki zai zauna lafiya ya ji dadin rayuwarsa,wanda kuwa ya ki binsu zai gamu da damuwa da tsaki a rayuwarsa.

Misalin wadannan ka’idodi:

_Allah ba ya kawo canji sai mutum/mutane sun canja salon rayuwarsu.
_Duk abinda ka aikata sakamakonsa zai dawo maka.
_Wanda ya dage ya yi kokari shine zai samu nasara.
_Zalunci sama da kasa shine yake ruguza al’umma.
_Allah bai yi mutane daya ba ,kowa da halinsa da yanayinsu,sai kowa ya tsaya iya matsayinsa.
_Kowane wuri akwai hanyar shigarsa.
Rashin fahimtar wadannan ka’idodi da aiki da su yana haifar da matsananciyar damuwa da ci baya a rayuwa.
4.SABON ALLAH TAALA
Sabo ko zunubi shine karya dokokin Allah Taala wanda ya haɗa da shiga hakkokin Allah da na bayinsa.
Kin bin umarnin Allah da bauta masa kamar yadda ya yi umarni,da aikata abubuwan da ya hana ,da zaluntar mutane da tauye musu hakkokinsu shine babban abinda yake haifar da bacin rai da damuwa.Saboda duk wanda ya hana wani barci tabbas shi ma ba zai yi barci ba ,ko ya yi sai dai da ido daya.
Saboda bin Allah Taala da bai wa kowa hakkinsa shine babbanaganin damuwa.
5.CIN HARAM DA ALMUBAZZARANCI
Bin hanyoyin yaki halal yaki haram da son Tara abin duniya ta kowane hali,da shirme da almubazzaranci da dukiya koda ta halal ce shine Musa babin fatawar mutane da dama cikin damuwa da bakin ciki da bacin rai.
Maganin wannan shine mutum ya zage damtse ya nemi halal kuma a yi amfani da abinda aka samu ta hanyar da dace ba kauro ba barna.
6.FIDDA RAI
Fidda rai daga samun sauki da canji daga Allah Taala babban zunubi ne kuma yana jawo matsananciyar damuwa da bacin rai.
Ya wajaba ga duk wanda yake cikin wani hali na damuwa ya cika zuciyarsa da kyakkyawan fata da zaton samun sauki da yayewar duk wani kunci da tashin hankali.Kuma mutum ya rabu da tsoro da fargabar abinda bai zo ba,saboda mai tsoron rashin lafiya ya fi kamuwa da ita,haka mai tsoron talauci yakan zama abokin kut da kut ga talauci.
7.CAMFI
Canji yana jefa mutane cikin damuwa.Misali camfa wata sana’a ko mace ko wurin zama wannan zunubi babba,kuma yana jawo damuwa da.gurbata rayuwa.
In dai mutum yana son zaman lafiya da kwanciyar hankali to lallai ne ya dogara ga Allah Taala ya yi fatali da camfe camfe da shashanci.
8.SHAAWAR HARAM
Sha’awar lalata ta maza ko mata tana jefa mai yinta cikin damuwa musamman idan bai samu damar cimma burinsa ba,In kuma ya samu ba zai taba gamsuwa ba saboda jini ba ya maganin ƙishirwa,haka dai za a yi ta rayuwa cikin damuwa da bacin rai.
Maganin wannan shine jin tsoron Allah da kaucewaduk wani kallo da tunani da abota da ƙawance na haram.
9.TSANANIN SON ABIN DUNIYA DA DOGON BURI
Wannan ma yana haifar da damuwa da sanya a bi kowacce hanya domin samun wannan ba kuma lallai ne a samu ba.
Maganin wannan shine takaita buri da baya baya da duniya.
10.HASSADA
Hassada ciwo ne babba kuma zunubi ne mai girma wanda yake hana mai yinta sakat a rayuwa.
Maganin wannan shine a guji hassada a wanke zuciya.
11.ZALINCI
Mutun ya yi zalunci ko a zalunce shi yana haifar da damuwa.
Maganin wannan adalci da hakuri.
12.TALAUCI
Yana jawo babbar damuwa kamar yadda kowa ya sani.
Magani shine hakuri da dagewa wajen neman halal da wadatar zuci.
In sha Allahu a rubutu na gaba zan kawo hanyoyin samun saukin musibu.
Allah Taala ya yaye mana dukkan damuwa duniya da lahira.