Wannan Shine Miji Na Gari

0
754

Duk wani miji a duniya ya na so da neman mace ta gari wacce a idonta akwai tausayawa, a wajenta akwai hutu da nutsuwa, a zuciyarta akwai so da kauna, kamar yadda shi ma yake siffantuwa da siffofin nagarta.

  • Miji na gari shi ne mai tsoron Allah a cikin maganganunsa da aiyukansa, ya na taimakawa iyalansa wajen samar da asalin tushen kauna, nutsuwa da girmamawa, wanda akansu musulunci ya gina zamantakewar aure.
  • Miji na gari shi ne wanda ya dauki Annabin Rahma sallallahu alaihi wa sallam abin koyinsa wajen kyautata mu’amala da iyalai, ta ya su aikin gida, debe musu kewa, sanya farin ciki da annashuwa a zuciyarsu tare da kauda kai daga rauni da rangwamen tunaninsu.
  • Miji na gari ya na sauraon matarsa, ya fahimci damuwa da bukatunta ya kuma baza tunani da kwarewarsa wajen magance matsaloli da damuwar farin cikin ransa.
  • Miji na gari ya na rikon matarsa a matsayin abokiyar rayuwarsa, rabin adddininsa, mahaifiyar ‘ya’yansa, ya na nuna mata kauna, kulawa da girmamawa, tare da karfafa mata gwiwa wajen aiyukan alkhairi.
  • Miji na gari ya na baiwa matarsa lokaci tare da tantance tsakanin hakkokin mahaifiya da na matarsa. Mahaifiya: kauna, girmamawa da biyayya. Mata: kauna, girmamawa da tausayawa.
  •     Matukar an samu mace ta gari a gidan miji na gari hakan zai basu damar zama da rayuwa ta gari, tare da samar da zuri’a ta gari wacce Annabin Rahma sallallahu alaihi wa sallam zai yi alfahari da ita. Allah jalla wa alaa ya na cewa:

Wal baladud dayyibu yakhruju nabaatuhu bi izni Rabbihi wallazi khabutha laa yakhruju illa nakida…” 6

RUFEWA

Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai baiwa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon shi zai sanya al’umma ta zama akan saiti da ci gaba wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma-Allah jalla wa alaa ya kiyaye-Dr. Muhammad Sani Umar ya na cewa:“Masu miyagun tunani sun dago kai, suna aiki dare da rana domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida.

Idan miji da mata suka sami hada kansu bisa turba ta musulunci to sai ka samu yayansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba akan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.

Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.

Subhanakallahumma wa  bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.

karanta yadda zaki mayar da gidan ki masarautar ki  ko ladubban tarewa a gidan miji ko Mahimmancin Aure a rawuwa domin sauki cekakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu