MUHIMMANCIN SANIN TARIHI (2)

0
953

Shi sanin tarihi sahihi yana taimakawa wajen fahimtar rayuwa da gujewa shirbici ko shaci-faɗi da kwaikwayo musamman ma sanin tarihin mutanen ƙwarai da suka gabata.

Koda yake shi tarihi ya kasu gida Biyu (2).

1. Tarihin wani zamani.
2. Tarihin wani mutum ko wasu mutane a wani lokaci.

Dukkanin waɗannan tarihi suna bukatar:

1. Ilmi sahihi da ruwaya sahihiya daga masana masu amana da tsoron Allah.
2. Yin adalci wajen yin bayanin abin da ya faru, ba tare da ɗaukar matsayi ko ra’ayi ba,
Hakan kuma ba zai tabbata ba sai an jiwo tarihin ko labarin ta fuska 3, musamman ma tarihin wata jama’a ko wasu ɗaiɗaikun mutane.

Fuska ta farko ita ce:

A. Ka ji labarin ta wajen wanda yake matuƙar ƙin abin (wannan zai yi maka bayani ne ta yadda zai ɓata abin, saboda ƙin sa da shi.

B. Ka samu tarihin ko labarin daga wajen wanda yake matuƙar son abin. (wannan ma zai yi maka bayani wajen gyara abin ko zuga shi saboda ƙaunar sa ga abin.

C. Ka ji tarihin daga wajen wanda ba ya ƙin ko son abin (wannan shi ne wanda zai yi maka bayani na adalci, saboda rashin ƙi ko son sa ga abin)
Zai yi maka adalcin ne saboda Allah (S.W.T) yana cewa:-

ولا يجرمنكم شنآن قوم عاى الا تعدلوا اعدلوا هو اقرب للتقوى
Ma’ana:

Kada rigimarku da wasu mutane ta kwashe ku, ta hana ku yin adalci, ku yi adalcin, shi ne mafi kusa da tsoron Allah.

Allah ya sa mu dace

labarin da ya wuceMUHIMMANCIN SANIN TARIHI (NA 1)
Labarin na GabaYadda Ake Sai Da Safe A Shimfiɗa