Yadda Ake Abincin Sallah Na Musamman

0
4363

Abincin sallah yana da matukar muhimmacin gaske, ga kuma farin jini. Saboda darajar wannan rana ta sallah, abinci ne dake da matuƙar daɗi, da ban sha’awa. Kowane gida, mai gida na ƙoƙarin siyayyar kayan abinci, domin a kyautata shi. Matar gida ma za ka tarar ta ƙure basirarta wajen yin haɗaɗɗen abinci.

Saboda haka girkin sallah na da buƙatar a ba shi kulawa ta musamman.

Akwai buƙatar tattaunawa tsakanin miji da mata. A fahimci karfin aljihu da irin abincin da aka fi so a yi, da wanda ya dace. da tanadin kayan ɗanɗano nau’ika daban-daban. Da kayan ƙamshin girki: citta da kanin fari da girfa da kori da Sauransu.

Haka kuma, in akwai hali, za a yi abin sha mai daɗi (juices). Musamman a Ƙaramar Sallah. A lokacin Babbar Sallah kuwa, za a yi kunun tsamiya. Kunun yana taimakawa sosai. Wajen hana ciki rudewa, saboda yawan cin nama. Kuma ba za a zauna da yunwa ba. Mata na ta fama da aikin Suya.

Akwai bukatar yin cincin mai ɗan yawa. Idan an zuba wa baƙi nama, sai a hada da cincin a gefen sa. Yana taimaka wa nama ya yi auki sosai.

YADDA AKE ABINCIN SALLAH

1- TUWON SHINKAFA MIYAR AGUSHI

TUWON SHINKAFA :
Za ki ɗora ruwa a tukunya yai zafi, ki wanke shinkafar tuwo ki zuba ta a ciki. Har sai ta dahu luguf. Ki cire ko matsa ki tabbatar ta wuce dahuwar normal shinkafa.
Sai ki sa muciya ki tuƙa ta da kyau. Ki rage wuta, ki bar ta zuwa wani lokaci. Ki bude ki sake tuƙa ta da kyau. Ki bar ta, ta turara sosai a hankali. Jimawa ki ƙara tukawa. Sai ki kwashe, ki yi malmala da ƙoƙo ki dinga sakawa a kwanuka. Ko kuma ki kwashe da cokalin kwasar abinci, kina sakawa a leda. Ki daure a saka a kuloli.

MIYAR AGUSHI
Za ki zuba mai, ki soya shi da albasa. Idan ya yi zafi, ki zuba markaɗeɗɗen kayan miya. Bayan sun soyu ki zuba ruwan nama, wankakken busasshen kifi, albasa, kayan dandano ( Maggi).

Idan ya tafasa, sai ki samu roba ki zuba agushi ki jiƙa shi da ruwan zafi. Sai ki juye shi cikin miyarki dake tafasa. Ki juya sosai. Kuma ki sa kayan ƙamshi. Bayan jimawa in kin ga agushin ya haɗu. Sai ki ɗauko wankakken ganyen ugu ki zuba. Ki juya, kuma ki ɗanɗana ko akwai buƙatar ƙara kayan ɗanɗano. Daƙiƙoƙi kaɗan sai ki sauke miyar ki daga wuta.2- FUNKASO:
Fulawa Rabin kwano
Alkama Rabin kwano
Yis cokali 2
Gishiri daidai.
Za a haɗa Fulawa da yis da gishiri. Sai a zuba ruwa a kwaɓa shi .Amma fa ka da yai ruwa, ya zama kamar kwabin fanke. Sai a saka mai Yai zafi. A dinga shafa mai a bayan Mara ta kwashe tuwo. Ana sa kwaɓi a faɗaɗa shi. Sai a dinga sawa a mai ana soyawa.

MIYAR TAUSHE : Za ki soya markaɗaɗɗen kayan miya, sai ki zuba ruwa da daddawa. Ruwa ya ɗan haura yadda kike bukatar miya. Domin miyarki ta dahu sosai . Idan ta tafasa, sai ki sa dakakkiyar gyaɗa ki juya. Ki zuba kayan ɗanɗano ( Maggi), gishiri, albasa, da garin citta, kanin fari. Bayan Jimawa ta dahu, sai ki zuba yankakken alayyaho (wankakke). ‘Yan daƙiƙoƙi kaɗan ganyen ba a barin sa yai ta shan wuta. Sai ki kashe wuta ki juye miya .

3 – WAINAR SHINKAFA :
Za ki wanke, ki jiƙa shinkafar tuwo. Ta wuni ko ta kwana ya danganta da irin lokacin da za ki yi abinci. A kai ta markaɗe. Idan an kawo sai ki zuba yis da  hoda da gishiri da sukari ki juya sosai. Ki rufe kwabinki cikin roba ko tukunya. Bayan ɗan tsawon lokaci, kullinki ya tashi sosai.

Sai ki sa kaskon waina a kan wuta. Risho, Gas, ko murhu. Wutar suyar waina kaɗan ake sawa. Ki zuba mai cokali ɗaya-ɗaya, a kowanne ramin kasko. Idan ya yi zafi, ki zuba babban ludayin abinci na kullinki. Ki na kallonsa idan ya yi sai ki juya ɗaya barin. Shi ma ki jira a hankali ya yi. Da haka za yi ta yi, har kullinki ya ƙare.

4 – ALKUBUS :
Fulawa kwano 1
Yis cokali 2
Gishiri daidai

Za ki sa wa Fulawa Yis da gishiri ki sa ruwa ki kwaɓa Fulawa. Kwabin ya zama kamar dai na fanke. Bai yi tauri ba . Sai ki bar shi zuwa jimawa ya tashi. Ki samu Leda a juya ta a dinga shafar mai ana zuba mata kwaɓi. A kulle a dinga Tarawa. A sa ruwa a tukunya ya yi zafi. Sai a juye ledojin duka a ciki. Wato kamar yadda ake alala. Idan ya dahu, a bude ledar, a yayyanka a ci da miyar taushe.

A ƙarshe dai yana da muhimmacin gaske. Mu ɗinga ƙoƙarin kyautata abinci. Tare da canja shi kala-kala. Ranakun bukukuwan sallah. Lokatai ne na sanya farin ciki. Yaran gida da dangi, da ma’aikatan gida, kowa ya ci, ya koshi. In dai da hali, za mu samu lada. Allah Ya na son ciyarwa.

Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ba za ku samu kyautatawa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da ku ka ciyar ko Mene ne, to Allah, gare shi masani ne (Ali-Imraan :92)

Allah Ya ba mu dacewa. Domin samun rubuce-rubuce da za su taimaka wajen inganta kowanne bangare na rayuwarmu. Sai a tafi www.wikiHausa.com.ng

 

labarin da ya wuceYadda Za Ka Zama Miji Nagari
Labarin na GabaYadda Ake Haɗin Salat Na Gargajiya
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.