Yadda Ake Banana Nutella Sandwish

0
925

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin banana nutella sandwich, ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

Abubuwan da ake buƙata

Biredi  slice -6

Mai cokali 3

Kwai 1

Siga cokali 2

Nutella

Ayaba

Madara ½ kofi

Yadda ake haɗawa:

  1. A buga Ƙwai, sugar da madara a cikin kwano mai zurfi.
  2. A tsoma bread a ciki haɗin ƙwai, madara da sauran su, sai a shafa nutella a kan sashe ɗaya.
  3. A shirya ayaba a kai, sai a ɗauko wani ɓarin breadin a ɗora.
  4. A gasa a toaster in ya gasu sai a cire.

Domin koyar yadda ake ice cream na ayaba danna wannan koren rubutun

labarin da ya wuceYadda Ake Ice Cream Na Ayaba
Labarin na GabaYadda Ake Caramelized Onion Grilled Cheese Sandwich