Yadda ake danderun nama sabon salo

0
653

Yadda ake danderun nama

Abubuwan hadawa
 1. Nama
 2. Albasa
 3. Attarugu
 4. Yaji
 5. Maggie
 6. Gishiri
 7.  Mai
 8. Spice da ki ke so ko ki ke da shi (na yi amfan da black pepper, nut meg da coriander powder)
 9. Seasoning da ki ke so
 10. Tafarnuwa
Yadda ake hadawa
 1. Za ki wanke naman ki sai ki ajiye agefe.

Ki daka nutmeg da black pepper in ba ki da dakakkiya.

 1. Ki nemi roba ki sa mai, attarugu, albasa, yaji, onga classic, tafarnuwa, maggie, spice and seasoning.
 2. sai ki zuba su nutmeg na ki da ki ka daka a cikin bowl din ki hada su.
 3. ki dauko naman ki kisa wuka kidan tsatstsaga ta.

Sannan ki dauko marinate naki na roban ki shafa ko ina a jikin naman kowani lungu lungu.

 1. Bayan kin gama marinating sai ki nemi tukunya ki sa ruwa sai ki sa murfin kwano a ciki sannan ki sa denderun na ki.
 2. ki nemi paper foil/ ko normal paper ki rufe naman naki. Ki barshi akan wuta ya nuna.
Karin Bayani
 1. Ba’a juya danderu hakanan zai nuna a low temperature.

Mafiya yawa a sallah muna yi da darraddare mu barshi a kasan garwashi har gari gari ya waye.

 1. Yawanci ana amfani ne da wuyar rago ko side na rago ko kuma cinyar rago wajen danderu.
 2.  Idan danderu ta nuna ki na tabawa za ki ga namar na barin jikin kashin alamun ya yi kenan.
 3. Kisa enough kayan hadi gun yin danderu su Maggie da sauransu. Akwai wani abu daya da danderu in ba ki sa enough maggie ba in ya nuna za ki ji taste din ya koma baya, to maggi bai jiba.  Saboda Hala, ki sa Maggi da seasonings suji amma kuma kada ki sa sosai.

KU KARANTA Yadda ake onion sauce