Yadda Ake groundnut sweet potato balls

0
75

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin groundnut sweet potato balls (groundnut cake) ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san:- groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin dan adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.

Abubuwan Buƙata

 1. Soyayyar gyada ¼ cup
 2. Dankalin hausa matsakaita
 3. Albasa a yanka kanana ko a jajjaga
 4. Curry ½ tablespoon
 5. Markadadden nama
 6. Sinadarin dandano
 7. Attaruhu guda biyar jajjagge
 8. Tafarnuwa
 9. Breadcrumbs 1 cup
 10. Kwai 3 (a fasa a kadashi)
 11. Man gyada na suya

Yadda ake hadawa

 1. A cikin kwano mai kyau a zuba dafaffiyar dankali sai a farfasata su fasu da kyau
 2. Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin dandano, curry, thyme da nama a juya a hankali
 3. A samu dan faranti a ringa diban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye
 4. A tsoma wannan ball cikin kwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe. Bon apetite

Domin koyon  Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie  danna nan.