Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie

0
202

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin groundnut, sweet potato pie ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san:- dankalin hausa na dauke da sinadarin bitamin vitaminB,C,E da vitamin K wanda yake yaki da kwayoyin cuta a jikinmu.

Abubuwan Buƙata

Yadda za’a haɗa pie                                           yadda za’ayi Fillings
 1. fulawa kofi 2                                                   Dankalin hausa guda ɗaya
 2. Baking powder babban cokali daya                   Gyada ½ kofi
 3. Man gyada Albasa
 4. Gishiri ½ karamin cokali                                  Attaruhu 2 matsakaita
 5. kwai guda daya (na shafawa kafin gashi)          Tafarnuwa 1
 6. Man suya                                                       Sinadarin dandano  guda1
                                                                        Thyme ½ rabin ƙaramin cokali
                                                                        Fulawa 2 cokali babba iyu
                                                                        Kori curry½ ƙaramin cokali

Yadda ake haɗawa

 1. A cikin tukunya a zuba gyaɗa a dafa ta dahu da kyau, idan ta dahu sai a saka dankali idan ta dahu sai a tace su a ajiye a gefe
 2. Cikin tukunya mara zurfi a zuba mai chokali biyu a zuba albasa a dan bata tsora sai a zuba attaragu tare da tafarnuwa da sinadarin dandano, thyme da kori(curry) a juya na minti 1-2
 3. A zuba dankali da gyada a dan juya
 4. A cikin qaramin kofi a hada fulawa da ruwa sai a zuba cikin wannan haɗin dankali da gyaɗa dake wuta sai abarshi ya dan hade na minti biyu kafin a kashe wuta.

Yadda zamu hada pie din mu

 1. A murza fulawa da man gyaɗa sosai sai a zuba ruwa da gishiri a murza ya murzu da kyau sai rufeshi na minti 5-7 domin ya haɗe da kyau
 2. Bayan wannan mintuna sai a sake murzashi, sannan ayi rolling a sami meat pie cutter in babu a sami dan roba ko kofi mai ɗan girma sai a ringa yanka fulawa dashi circle-circle
 3. A zuba wanna hadin gyaɗa a da dankali a tsakiya sai a a shafa ruwan fulawa a gefe sannan rufe a danna cokali mai yatsu
 4. A shafawa pie din ruwan kwai
 5. A gasa na minti 30 ko sama ko kuma idan yayi ruwan ƙasa wato golden brown.