Yadda Ake Hadin Kayan Kamshi

0
607

Assalam alaykum
Barkanmu da sake kasancewa cikin sabon shirinmu na girka girken WikiHausa Wanda muke koyarda kayatattun abinci namu na gida Najeriya dana ketare Tare da bayani akan lafiyarsu a jikin dan Adam cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat shettimah… A yau zamu kawo muku yadda ake Hadin kayan kamshi na musamman, ku biyo ni domin mu koya tare…

Yadda Ake Hadin Kayan Kamshi.

KO KUN SAN: Saka kayan kamshi cikin nama na hana Karni kuma yasa nama yayi kamshi na musamman.

Yadda Ake Hadin Kayan Kamshi.

Abubuwan da ake bukata:

Gyadar miya (Nutmeg)
Citta (ginger)
Cadarmom(hab’al)
Cumin
Coriander leaf
Masoro (black pepper)
Kaninfari (cloves)
Kirfa (cinnamon)
Tafarnuwa (garlic)
Bushashshiyar Albasa (dried onions)

Yadda ake hadawa:

1. Za’a gyara wannan kayan kamshin acire datti sannan a daka ko a niqa da blender.
2. A tankaDe shi, sai a sami leda juye aciki sannan a saka a roba mai murfi. HAKAN NA SA KAMSHIN BAZAI FITA BA NA TSAHON LOKACI.