YADDA AKE KUNUN GYADA MAI GASARA

0
140

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin KUNUN GYADA MAI GASARA ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

Abubuwan buƙata
  1. Gasarar gyada (groundnut butter)
  2. Gero
  3. Chitta[optional]
Yadda ake hadawa
  1. A jika gero da daddare zuwa safe sai a saka chitta a kai markade in an dawo a tace a fitar da dusa.
  2. A debo gasarar gyada sai zuba wadataccen ruwan da zai dama kunu. A juya da kyau a sa rariya a tace acikin tukunya mai zurfi a dora akan wuta.
  3. Idan gasarar gyadar ya tausa sai ajuye a cikin gasarar gero a juya. Sai a zuba lemon tsami, ko tsamiya ko dan tsami
Domin sanin yadda ake kunun gyada danna nan