YADDA AKE KUNUN GYADA

0
180
Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin  kunungyada ku biyoni a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san:-kunun gyada mai shinkafa na bada kuzari wanda carbohydrate ke badawa sannan gyada na ba anadario vitamin B3 (niacin) wanda ke taimakon breaking down carbohydrates into energy.
Abubuwan Buƙata
  1. Gyada (kofi daya ) (a soyata sannan a bakace)
  2. Shinkafa [kofi daya]
  3. Chitta [optional]
  4. Lemon tsami [to taste] [har sai yaji]
Yadda ake hadawa
  1. A zuba gyada cikin tukunya mai dan zurfi sai a soya ta sama sama asai a juye a bakace ta a fitar da fatar tas
  2. Sannan cikin bokiti ko roba mai zurfi a zuba shinkafa da gyada,chitta in ana bukata sai a kai markade.
  3. Idan an markado sai a saka abin tata a tace.
  4. Sai cikin tukunyar mai zurfi sai a zuba gasarar kunun ayi ta juyawa har sai yayi kauri
Sai a zuba lemon tsami a taba a ji in tsamin yayi ko bai yi ba.ayi a hankali wurin zuba lemon tsamin kar yayi yawa. Kuma kar yayi kaɗan saboda in yayi kaɗan kunun zai iya tsinkewa
Domin sanin yadda ake abincin yara danna nan