Yadda ake onion sauce

0
653

 

Abubuwan hadawa

 1. Albasa
 2. Koren tattasai
 3. Tarugu
 4. Tattasai
 5. Kayan kamshi
 6. Maggi
 7. Kwakwamba (cucumber)
 8. Butter ko man gyada
Yadda ake hadawa
 1. Ki dauko albasar ki gyara ki yanka ta kanana sai ki wanke ki tsane shi a matsani.

Ajiye a gefe dauko koren tattasai ki yanka shima ajiye a gefe.

Dauko tarugu ki yanka kanana, ajiye a gefe.

 1. Ki daura non stick pan akan wuta ki sa butter ki yanka albasarki ki soya sama sama,

sai ki dauko tarugu ki sa ki soya sama sama shima, sai ki dauko kayan kamshi ki sa, maggi (iya dandano da zai miki),

sai ki dauko yankakken albasa (dama kin yanka shi dadan dama) ki sa.

 1. A nan sai ki sa ruwan dumi kamar cokali 4 (tbsp) ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya ragu.

Sannan ki dauko koren tattasai da cucumber ki sa ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye sai ki sauke ki zuba a plate.

Ku karanta Yadda ake vegetable macaroni