Yadda ake soyayyiyar Gyaɗa mai gishiri

0
262

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda kayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a sauƙaƙe tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin soyayyiyar gyada mai gishiri ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san:- soyayyiyar gyada na saurin narkewa a jikin dan adam.

Abubuwan Buƙata.

  1. Gyada rabin mudu (bararriyar gyaɗa/mara bawo).
  2. Ƙasa (kamar kofi biyu). Yashi ko toka.
  3. Gishiri chokali uku

 Yadda ake hadawa.

  1. A tsince gyaɗa mara kyau, ko a bakace gyadar domin fitar da marasa kyau. Sannan a wanke gyaɗar ta fita fes.
  2. A cikin roba mai zurfi a zuba ruwa, ɗan gishiri da kuma gyaɗar sai a barta kamar na awa 3-4 bayan awannin sai a tace a busar dashi a inuwa ko rana.
  3. A zuba ƙasa acikin tukunya mai zurfi idan ƙasar tayi zafi sai a zuba gyaɗar cikin ƙasar ayita juyawa har sai gyaɗar ta gasu da kyau.
  4. Sai a sauke a raba gyaɗar da kasa sannan a barta ta sha iska.

Domin koyar Yadda Ake Soyayyiyar Taliya danna wannan link din