Yadda Ake Turaren Daki Na Musamman

0
2683

Turaren daki na ruwa mai dadin kamshi, ya na sa dakunanmu su zama na Musamman.

Babu shakka dakunan mu na da bukatar kulawa ta Musamman, Domin su zama wajen hutawarmu tare da mazajenmu. Mu dinga tsaftace su, kuma mu dinga yawan sa turaren daki na Musamman akai-akai.
Hadin wannan turare yana da saukin hadawa. Kuma da kudinki dan kadan za ki hadashi.

KAYAN HADA TURAREN DAKI NA BAKHUR :

Ruwan Bakhur
Ambur
Turaruka Madarori: Sk, Nasis , Sultan.

Za ki juye ambur a roba. Sai ki dake ambur shima ki zuba aciki. Sai ki juye madarorin turaren Sk , Nasis , sultan . A dinga yarfashi a kafet , dardumar sallah da shimfidar gado.

KAYAN HADA TURAREN DAKI NA RUWAN Ss:

Turaren ruwa na Ss
Turaren kafi-kafi
Madarar ambur
Ambur dakakke
Itacen Demask nikakke
Kafur

Idan ki ka hadasu sauran sai ki zuba cikin Ruwan turaren Ss. Ki juya su hade sosai. Sai ki zuba madarar ambur. Sai ki rufesu cikin mazubi. Ki dinga yarfawa a shimfidun falonki da daki. Dardumar sallah , harma da jikin kujerunki.

Domin karanta yadda ake turaren wuta danna koren rubutu