Yadda ake yin kuli kuli

0
101

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin kuli kuli ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san:- kuli-kuli abincin yara ne ko ince yara nason Kuli Kuli kuma ana iya sarrafata ta hanya yin garin quli-quli sannan ya zama ingredients din abincin kowa.

Abubuwan Bukata

 1. Gunda
 2. Gishiri
 3. Citta
 4. Barkono
 5. Sinadarindandano
 6. Sugar

Yadda ake hadawa

 1. A soya gyada sama-sama sai barzata tabbatar an tsince an barza (babu mai bori kwata-kwata).
 2. A fitar da baqin gyada, domin tana saka daci
 3. Sai ka kai a markada kar a zuba ruwa kamar kullin gyada (peanut butter)
 4. A jiqa
 5. A tsince gyada, a cire mai bori sannan a cire bakin gyadar sai a soyata sama-sama karta qone
 6. A mar kada gyada dan gishiri, citta ko in mai sugar za’ayi sai an dan saka sugar.
 7. A tace ruwan tsamiya a barshi ya kwanta sai a juye abu mai kyau.
 8. Bayan an markada gyada, sai a sakata cikin kwano mai zurfi a zuwa wannan ruwan tsamiya kadan ayita juyawa da muciya ko cokalin katako har sai anga mai ya fara fitowa.
 9. Sannan za’aga gasarar ya curewa ko ince yana dunkulewa. Sai a tsiyaye mai sannan a cura qulin a soyata.

Domin koyon Yadda ake yin dakuwa danna nan