Yadda AkeTherapeutic Food (abincin yara)

0
205

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake Abinci yara (therapeutic food) ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san:- yara masu cutar yunwa (tamowa) idan ana basu wannan zai kara musu kuzari da kumara a jikinsu.

Abubuwan Buƙata

 1. Gyaɗa (kofi biyu)
 2. Waken suya (kofi biyu)
 3. Dawa (kofi shida)
 4. Siga
 5. Madara (in ana buƙata).

Yadda ake hadawa

 1. A soya gyaɗa a busheta sannan a niƙa
 2. A soya waken (soyabeans) shima a niƙa
 3. Dawa itama a soyata sannan a niƙa
 4. Cikin roba mai kyau a hada dukkanin garin (wake soya, dawa da kuma gyaɗa ) a juya da kyau sai a sami leda mai kyau a juye a cikin sannan a saka a roba mai murfi a rufe. Duk sanda za’ayi sai a diba.

Yadda ake hada kunun

 • A dora tukunya mai zurfi sannan azuba ruwan zafi kaɗan yadda zai isa (kamar talge).
 • A dan kofi ko roba a debi garin kunun yara sai azuba ruwa a cikin dan kadan a dama.
 • Idan ruwan ya tausa sai azuba wannan gasarar kunun a cikin ruwan ayita juyawa har sai yayi kauri
 • Za’a iya saka madara domin ƙarin daɗi kuma za’a iya sha a haka.

Domin Yadda Ake Gasarar Gyada (Peanut Butter) danna nan