Yadda Za a Ci Jarabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Ciki Sauki

0
542

A duk Lokacin da ka samu kanka cikin wani hali na matsatsi iri-iri.
To ka tuna daman can Allah Ya na jarrabar bayinsa da masifu daban-daban.

Allah Ya ce :
“Wallahi sai mun jarraba ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da tawayar dukiya, da asarar rayuka da na kayan marmari, kuma albishir ga masu hakuri”.
( Baqara:115).

Ka ga tunda mun fahimci kowanne irin tsanani daga Allah ne. To, ka ga mun san babu mai ya ye mana sai Allah Madaukakin Sarki.

Menene abin yi kenan?

Abin yi shine mu rungumi wannan kaddara, da yin hakuri , da ko yi da yadda Annabi (S.A.W) ya ce mu yi.

Jarrabawa na iya zama mabanbanta a tsakaninmu. Wani rashin iyaye, wani cuta, wani talauci, wani rashin ‘ya’ya da dai sauransu.

Wani Lokacin kuma ya zama Annoba ce da Allah Ya jarrabi dukkanin al’umma. Wato kamar ciwon sarkewar numfashi ( Corona).

Shi Musulmi duk abin da ya same shi na sharri da wahala ba za ka sameshi ya na raki ba. Kuma yai ta mita ko lakanawa wani shi ya ja masa. Ko da ya ke rauni irin na dan Adam ba’a hana Mutum bakin ciki ba. Amma dai zai zama mai Dogaro ga Allah .

MATAKAI CIN JARRABAWAR BALA’IN DA YAI TSANANI
 • Mu Kaskantar da kawunanmu. Mu tuba , muyi nadama. Mu yawaita istigfari .
 • Mu yawaita karatun Qur’ani.
 • Mu bincika tsakaninmu da iyayenmu mu gyara. Mu dinga kyautata musu.
 • Ma’aurata su gyara tsakaninsu.
 • Mu yawaita sadaka.
 • Mu yawaita addu’a Allah Ya yaye Mana. Ya kawo mana mafita.
 • Mu yawaita : Hasbunallahu wa Ni’imal wakeel.
  Lahaula wala quwwata illa bilLah.
  La’ilaha illa anta Subhanaka inni kuntu minaz zalimn.

A karshe mu sani mai sauki ne awajen Allah Ya yaye Mana kowanne irin Bala’i. Saboda haka mu gaggauta gyara tsakaninmu da Mahaliccinmu. Sannan kuma ga dukkanin jarrabawa irin ta Annoba.
Mu bi shawarar Malamai, da shugabanni , da Ma’aikatan lafiya. Da bin wadannan in shaa Allahu sai ka ga mun yi Nasara. Mun ci jarrabawar bala’in da ya tsananta cikin sauki.

WalLahu A’alam .
Duba yadda ake tsaftace baki .

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here