Yadda Za Ki Koyawa Mijinki Ko Matarka Wasanni

0
2087

Yadda Za Ki Koyawa Mijinki Ko Matarka Wasanni
Yadda Za Ki Koyawa Mijinki Ko Matarka Wasanni

Wasannin ma’aurata Iri-iri ne . Su na kara dankon soyayya da samun biyan bukata. Su na sa biyayya har ma da mallaka

Rashin su kuwa ,na sa daya daga cikin ma’aurata ya zauna cikin sha’awa, da kunci, da rashin natsuwa, har ma ya kai ga kiyayya. Ko ma rabuwar ma’aurata.

Ire-iren wasanni sun hada da shafa wasu sassan jiki ahankali. Yin sumba ( Kiss) na labba, da runguma , da da yin amfani da baki/ harshe a wasu sassan jiki. Da hura iska a kunne. Da dai sauransu.

Ammafa runguma da sumbata ba za su yiwu ba. Sai dai da wanka, wanke baki da fesa turare.

Idan miji/ ko mata ta ji ka na wari. Za ka ga kawai ta na kin kusantarka balle wasanni.

Idan aka jarrabeka da Mijin da bai iya wasa ba. Ko matar da ba ta iya wasa ba. To ya kan sa aji angaji da juna.

HANYOYIN KOYAR DA WASANNI

1- Banda bata rai, da korafi , da nunawa wanda baya wasan shi/ ita ‘yar kauye ce.

2- Kai / ke mai koyar da wasan zai fara ne da maganganu masu gayyato sha’awar mijinki. Da yaba masa yana burgeki a shimfida ko da ba hakan ba ne kuwa.

3 – Mai koyarwar ya dinga dauko hannun miji/ mata ya na sawa a inda ya ke so a jikinsa. Domin shafa…

4 – Ki kai abin da ki ke so ga bakin mijinki. Kai ma ka kai abin da ka ke so ga bakinta..

5 – Ba da labarin irin dadin da ake ji da akai Miki/maka abu kaza.

6 – Bada Umarni ammafa cikin lumshe ido da sigar buguwa/ maye na kalar wasan da ake so ga mijinki ko matarka. Kallon wannan yanayin na ka zai sa nan da nan ayi abin da aka umarta.

Zai fi kyau ga ma’aurata ma akowanne lokaci za ku rabu ko ku ka hadu. To afara da sumbatar juna.
Nana Aisha ta ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya na sumbatar matarsa idan zai fita. ( Abu-Dawud).

A karshe ya zama tilas ga ma’aurata su kula da gabatar da wasanni kafin shimfida. Domin dayawa ma’aurata ba sa samun gamsuwa in ba bu wasanni. Hakan na haifar da matsaloli da yawa ga su Ma’aurata.
Wallahu A’alam

Domin karanta yadda ake maraba da maigida ko yadda ake da maigida lokacin al’ada