Yadda Za Ki Yi Wa Namiji Mai Shiru Shiru

0
1480

Wani Namijin halittace shiru-shirunsa . Ba damar canja shi. Ba zai miki hira ba, kuma ba zai saurari hirarki ba.

Sai ki yi nazari ki fahimci ke kadaice ba yawa hira ? Ko ke kadai ce bai damu da ya saurara ba?
Idan ako ina ma haka ya ke baya son magana. Sai ki yi hakuri. Rashin miki hira ba zai hana ki samun Rahamar Allah ba.
Sai ki daina kallo da damun kanki akan hirarsa.
Ki mayar da hankalinki akan sauran halayensa na kirki. Abubuwa dayawa Wadanda wasu matan dayawa ba su samu ba. Ke kina samu , Kuma ki godewa Allah .

IDAN MIJINKI MAI MAGANA NE ….

Idan mai magana ne ke ce kadai ba ya son yi da ke.
Na farko ki koma ga Allah wajen yawaita istigfari.
Na biyu ki yi ta nacin addu’a . Tashi qiyamul layl akan Allah Ya warware miki matsalarki.
Na uku : ki yi tunani daga wajenki za’a samu gyaran ko kuma daga wajensa ne?
Wato ko ba ki fahimci irin hirar da ya fi so ba?
Ki yi nazarin rayuwarsa. Misali :
Mai son labarai: Kullum ya na karanta jarida. sai kina karanta jaridu, da sauraron labarai a radiyo.
Idan kun zauna sai ki fara bashi sabbin labarai wannan rana .
Mai kiwon kaji ne sai kin karanci. Ire-iren kaji , da abincinsu, da magungunansu.
Dan Kwallo : Sai kin karanci qungiyoyi ball. Da labaran’yan kwallo da suke tashe ayanzu.
A karshe dai yana da muhimmanci mace ta karanci irin sana’ar mijinta. Da mafi yawan abubuwa da suka shafi mijinta. Hatta labarin rayuwarsa . Zai taimaka sosai wajen rage yawaita matsaloli.
Wallahu A’alam .

Domin karanta yadda ake da maigida lokacin al’ada ko yadda ake shagwaba mai gida lokacin hutu