Menene Amfanin Zumunci

0
922

Sadar da zuminci,shine ziyarar yan uwa da dangi da abokai na alkhairi da taimakonsu da agaza masu”.

Annabi s.a.w ya bayyana mana sadar da zuminci hanyace ta samu arziki da rayuwa mai dadi anan duniya da Lahira.

Sai yace:
(ﻣَﻦْ ﺳَﺮَّﻩُ ﺃَﻥْ ﻳُﺒْﺴَﻂَ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﺭِﺯْﻗُﻪُ، ﺃَﻭْ ﻳُﻨْﺴَﺄَ ﻓِﻲ ﺃَﺛَﺮِﻩِ ، ﻓَﻠْﻴَﺼِﻞْ ﺭَﺣِﻤَﻪُ)

Duk wanda yake son Allah ya yalwata arzikinsa kuma ya tsawaita rayuwar sa, to
ya sadar da zumincinsa).
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏) 2067 ‏( ،ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏) 2557 ‏( ،ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏) 1693 )

Awani Hadisin yana cewa:
(ﺍﻟﺮَّﺣِﻢُ ﻣُﻌَﻠَّﻘَﺔٌ ﺑِﺎﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺗَﻘُﻮﻝُ ﻣَﻦْ ﻭَﺻَﻠَﻨِﻲ ﻭَﺻَﻠَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﻣَﻦْ ﻗَﻄَﻌَﻨِﻲ ﻗَﻄَﻌَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪ)

(Zuminci yana rakaye ajikin al’arshi yana cewa ya Allah ka sadar da wanda ya sadar dani ka yanke wanda ya yanke ni).
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏) 5989 ‏( ﻣﺴﻠﻢ ‏)

Mu hadu a darasi na gaba insha Allah.